November 8, 2022

JAGORA NA, NA ADDINI HUJJATUL ISLAM WAL MUSLIMUN SHEIKH MUHAMMAD NUR DASS (H)

JAGORA NA, NA ADDINI SHEIKH MUHAMMAD NUR DASS (H).

 

√ Daga cikin kokarin wakilin Sayyed Ali Khamnei (DZ) janibin shari’a wato Samahatu Sheikh Nur Dass (H) a Nigeria akwai:

~ Assasa Mu’assasar RASULUL A’AZAM FOUNDATION (RAAF) Mu’assasa ce ta Shi’a Zallah tare da yima wannan Mu’assasar rijista a hukuman ce.

~ Rasulul A’azam Foundation (RAAF) Mu’assasa ce dake bude makarantun Hauzozin ilimi da markazozi dan yada addinin musulunci cikin shi’anci tsantsa.

~ Tana da Makarantun Hauzozi a jihohi daban daban a fadin Nigeria kuma duka makarantu ne masu rijista.

~ Tana da kebantaccen sashe na abinda ya shafi kira da tabligh, wannan sashe ya tara muballigai dayawa a karkashin shi, duka dan Isar da sakon Ahlul-bayt (AS) a fadin Nigeria, Shugaban wannan sashe shine Hujjatul Islam wal muslimin Shekh Bashir lawal kano, wanda ake masa laqabi da Sautush~shi’a.

~ Haka nan wannan shugaba kuma wakilin Sayyed Ali Khamnei (DZ) ya assasa babban Hauza a cikin birnin kano, sunan wannan Makaranta HAUZATU BAQIRUL ULUM wanda shi ke jagorantar wannan makaranta, an samu daga ‘Dalibai wadanda suka sha karatu suka fita suma Suna taimakawa a ‘bangaren tabligh.

√ Daga cikin kokarin da yayi a bangaren siyasa da janibin jama’a kuma:

1. Yada abinda ya shafi wayewa tsakanin jama’a da abinda ya shafi siyasa, yayi haka ne wajen farkar da ‘yan shi’ar kasar wajen shiga cikin al’amuran daya shafi qasa kuma ayi dasu sbd suma ‘yan kasa ne.

2. Wayar da kan ‘yan shi’a akan abinda ya shafi mahimmancin siyasa, yin zabe da fitowa a zabe su kamar sauran ‘yan qasa da sauran Kungiyoyi.

3. Kokarin shi na hadin kai tsakanin Qungiyoyin Musulunci da ‘yan shi’a suma a junan su, ya taka rawar gani a wannan janibi.

4. Gusar da mummunan ganin da hukuma take yiwa ‘yan Qungiyar daga ‘yan tawaye kuma masu taka doka, zuwa ‘yan kasa na gari masu kishin kasar su.

::: Akwai kuma kokarin shi na tarwatsa shirin wahabiyawa da suke na kokarin ‘bata sunan shi’anci a cikin kasa, tare da sauran daukan mataki da suka.

SHARE:
Makala 0 Replies to “JAGORA NA, NA ADDINI HUJJATUL ISLAM WAL MUSLIMUN SHEIKH MUHAMMAD NUR DASS (H)”