Iran: Masu ta da tarzoma na son rage tasirin Iran ne – Jagora

Jagoran juyin juya halin kasar Iran, Ayatullah Ali Khamene’I ya bayyana cewa makiya na neman tarwatsa cigaba da tasirin Iran ta hanyar sabuwar tarzomar da suka tayar a cikin kasar.
Ayatullah Khamene’I ya bayyana hakan ne a garin Tehran, babban birnin kasar Iran a yau Litinin a yayin da yake ganawa da wasu ayarin jama’a daga garin Qom a taron tunawa da ranar zagayowar wata tarzomar da aka tasar a Qom na nuna kin jinin gwamnatin da ke da alaka da kasar Amurka ta Pahlevi ta 1978.
Jagora ya ce masu zanga-zangar ba su hau titi don nuna matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da ita sabida takunkumin kasashen yamma ba.
Ya bayyana cewa tabbas kasar kam na fama da matsin tattalin arziki a yau, sai dai kuma ya bayyana cewa wadannan matsalolin ba zasu kau ta hanyar tarzoma ba sai dai kawai suna so su kawo tsaiko a lamarin tasirin kasar. Ya kuma kara da cewa makiya na waje na sanya hannu cikin lamarin ta da tarzomar kana kuma kasashen turai na kara rura wutar tarzomar ta hanyoyi daban daban.
Jagora ya ce kafofin yada labaran yamma na bata fuskar kasar ta Iran ta hanyar yada farfaganda da kage-kage. Ya kuma ce abinda masu zanga-zangar suka yi cin amanar kasa ne kana kuma ya kira hukumomi da su dau matakan da suka dace kan duk masu cin amanar kasa.
Masu zanga-zangar dai sun fara ne a yankokin kasar ta Iran tun sanda Mahsa Amini yar shekara 22 ta rasa ranta a asibiti a ranar 16 ga watan Satumbar shekarar da ta gabata biyo bayan faduwar da ta yi a ofishin yan sanda kwanaki uku kafin mutuwarta a Tehran.
Rahotannin likitoci dai sun nuna cewa mutuwar Mahsa ya faru ne sanadin yanayin rashin lafiya da ke damun ta sabanin zargin da ake na dukan da yan sanda suka yi mata.
Tarzomar masu zanga-zangar dai ta haifar da mutuwar gomomin mutane da kuma jami’an tsaro, kana kuma ya bude hanya ga yan ta’adda na aiwatar da ayyukan ta’addacin su. Cikin watanni uku da suka gabata, yan ta’adda sun kona wurare uku kana kuma sun ci zarafin mutane dayawa daga mambobin Basij da kuma jami’ai wanda hakan ya kai ga mutuwar wasu daga cikin su.
Kasashen Amurka da Turai da kuma abokan su sun nuna goyon bayan cigaba da tarzomar a fadin Iran.