August 19, 2023

​Jagora: Makiya Suna Son Bata Sunan IRGC Da Basij A Duniya

 

Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa makiya suna son bara sunan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar wato IRGC da kuma rundunar sa kai ta ‘Basij’ a duniya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a ranar Alhamis a lokacinda yake ganawa da majalisar koli ta kwamandojin IRGC a gidansa nan Tehran.

Jagoran yana kara da cewa makiya basu da wata hanya ta bata sunan dakarun na IRGC sai fadin karya da kuma yada farfaganta na kariya a kansu. Ya kuma kara da cewa dakarun IRGC mayaka ne wadanda suke iya aiwatar da ayyukansu kamar yadda ya dace kuma babu wata rundunar sojoji a duniya wacce take iya yin abinda IRGC take yi.

Daga karshen jagoran ya bayya rundunar IRGC a matsayin runduna wacce ta bambanta da duk rundunar sojojin a duniya musamman a kasashen da aka yi juyin juya hali, wajen biyayya ga gwamnatin tsakiya ta kasa wacce bata sabawa manufofin kafata tun asali. Ba kamar yadda rundunonin sojojin kasashen Faransa da Rasha bayan nasarar juyin juya hali a kasashensu ba.

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Jagora: Makiya Suna Son Bata Sunan IRGC Da Basij A Duniya”