March 15, 2023

Jagora : Dole Ne A Hada Kai Domin Karya Tasirin Takunkuman Amurka Da Kawayenta

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bukaci hadin kasashen dake fama da takunkuman Amurka da kawayenta a wani mataki wanda a cewarsa shi ne zai karya tasirin wadanan takunkuman na zalinci da aka kakaba masu.

‘’Dole ne wadanan kasashen su hada karfi da karfe wajen ruguza wadannan haramtatun takunkuman’’ inji jagoran.

Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko, wanda ya ziyarci Tehran ranar Litinin.

Kafin hakan dama Kasashen Iran da Belarus, suncimma yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Jagora : Dole Ne A Hada Kai Domin Karya Tasirin Takunkuman Amurka Da Kawayenta”