Iyaye Da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya Ta Yi Watsi Da Karin Kudin Makaranta.

Iyaye sun fara kokawa da karin kudin makaranta da wasu jami’oin kasar nan suka yi wasu kuma ke shirin yi, ita kuwa kungiyar daliban jami’oin kasar ta ce bazata sabu ba.
Kungiyar daliban ta ce batun karin kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki zai kasance wata babbar matsala ga daliban da kuma iyayensu.
Tuni kungiyar ta ce ka kafa wani kwamiti a shiyoyin Najeriya don su zauna da jami’o’in game da yadda za a shawo kan al’amarin.
Sanarwar da wasu jami’o’in Najeriya suka fitar cewa daga zangon karatu na gaba a kwana da sanin an kara kudin makaranta, ya yi matukar jefa wasu iyayen da dalibai cikin zukumi da jimami, saboda a cewarsu dama da kyar da jimibin goshi suke biyan kudin makarantar na yanzu.
Wani uba ya shaidawa BBC cewa ya kadu matuka da ‘yar shi ta kawo mishi takardar batun karin kudin jami’ar.
”’Ya ta da ke jami’ar gwamnati da ke Dutse a jihar Jigawa ta kawo min takardar kuma an rubanya kudin har sau biyu, gaskiya gwamnati ya kamata ta saurari kukan mutane, abinci ma na neman gagarar mutane.
Kullum su na dabbaka batun yin ilimi, to amma da alama wasu sai dai su hakura da karatun saboda ba su da hanyar biyan kudin karatun.”
Suma daliban sun ce sam-sam wannan matakin bai yi dai-dai ba, inda suka kafa kwamitoci a shiyoyin Najeriya don zama tare da samun matsaya da jami’o’in da suka kara kudin ko suke shirin karawa.
Kungiyar malaman jami’oin ta ASUU tace da ma ta san za a rina, saboda kudaden gudanarwa da jami’o’in suke karba daga gwamnatin tarayya basa isa.
Bayanai na cewa tuni wasu jami’oin suka kara kudin makarantar da fiye da kashi dari, inda karin zai fara aiki a zangon karatu na gaba, sannan wasu da dama ciki har da jami’ar tarayya da ke Dutsen jihar Jigawa suke kan tattauna yadda za su yi kari.