February 22, 2024

Isra’ila Zata Kayyade Adadin Masu Zuwa Sallar Juma’a A Masallacin Kudus

Isra’ila ta sanar da cewa za ta kayyade adadin Musulman da za su rinka zuwa Sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa a lokacin watan Ramadana.

Ministan tsaron kasar Itamar Ben-Gvir a ranar Talata ya ce yunkurin da ya yi na haramta wa akasarin Musulmai Sallar Juma’a hakan bai yiwu ba sakamakon Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da hakan.

Sai dai ya ce duk da hakan za a kayyade adadin mutanen zuwa mutum dubu 40 ko dubu 50.

Rahotanni sun nakalto Ministan yan sandan kasar na cewa akwai yiwuwar masallacin ya kasance wurin da za a gudanar da zanga-zanga.

Masana da dama sun bayyana fargaba game da wannan matakin wanda suka ce zai iya kara rura wutar rikicin da ake ciki a yankin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Isra’ila Zata Kayyade Adadin Masu Zuwa Sallar Juma’a A Masallacin Kudus”