March 22, 2024

Isra’ila” ta kuduri aniyar tura sojojinta zuwa birnin Rafah da ke kudancin Gaza,

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya ce “Isra’ila” ta ci gaba da kuduri aniyar tura sojojinta zuwa birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Falasdinawa sama da miliyan 1 suke mafaka, kuma za ta yi hakan ba tare da goyon bayan Amurka ba idan ya zama dole.

Netanyahu ya fada a cikin wata sanarwa da ya shaidawa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da ya ziyarce shi cewa “Ina fatan za mu yi hakan tare da goyon bayan Amurka, amma idan har aka ki haka – mu kadai za mu yi.”

Blinken ya gana da Netanyahu a tattaunawar da ke da nufin tabbatar da karin abinci a Gaza.

© Al-mayadeen

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Isra’ila” ta kuduri aniyar tura sojojinta zuwa birnin Rafah da ke kudancin Gaza,”