May 30, 2024

Isra’ila” ta yi amfani da makaman da aka yi a Amurka a kisan da tayi a Rafah,

Kamfanin dillancin labaran CNN ya bayar da rahoton cewa, “Isra’ila” ta yi amfani da makaman da aka yi a Amurka a kisan kiyashin da ta yi wa wani sansanin tanti a Rafah, wanda ya kashe Falasdinawa 45 da suka rasa matsugunansu, kamar yadda CNN ta ruwaito, ta nakalto wasu hotuna daga wurin.

Binciken na CNN ya samo asali ne daga faifan bidiyo da aka nuna a wurin harin na ranar Lahadi, wanda ya nuna wutsiyar wani bam mai suna GBU-39 da Amurka ta kera, wani binciken da wasu kwararrun makaman fashe hudu suka tabbatar.

CNN ta kuma lura cewa jerin lambobin da suka rage a cikin makaman sun yi daidai da na wani kamfanin kera sassan GBU-39 na California.

Rundunar sojin Isra’ila ta yi ikirarin cewa ta kai hari a wani fili da mayakan Hamas ke da su, lamarin da ya haddasa fashewar wani abu da ya janyo gobara da sauri ta bazu zuwa tantunan da ke kusa. An lalata sansani a yankin Tal al-Sultan na Rafah, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 45 tare da jikkata kusan 200.

 

© Al-mayadeen

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Isra’ila” ta yi amfani da makaman da aka yi a Amurka a kisan da tayi a Rafah,”