April 7, 2024

Isra’ila” ta rufe ofisoshin jakadancinta 27 saboda fargabar ramuwar gayya na Iran

Jaridar ahlulbaiti ta ruwaito daga tashar Al-Mayaden ta larabci cewar: Mashawarcin Jagora addini na Iran sayyed Ali Khamenei kan harkokin soji, Manjo Janar Yahya Rahim Safavi ya yi magana game da matakan da “Isra’ila” ta dauka a lokacin da suke jiran martanin Iran kan harin da Isra’ila ta kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus a farkon makon nan.

Safavi ya bayyana cewa, “Isra’ila” ta rufe ofisoshin jakadancinta 27 a yankin saboda fargabar ramuwar gayya na Iran, ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana jiran lokacin da ya dace domin mayar da martani.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Isra’ila” ta rufe ofisoshin jakadancinta 27 saboda fargabar ramuwar gayya na Iran”