June 2, 2024

Isra’ila ta kame yar jaridar Falasdinawa a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke murkushe ‘yan jarida

Jaridar ahlulbaiti ta ruwaito daga tashar Al-Mayaden ta larabci cewar.

Sojojin gwamnatin  Isra’ila sun kama wata ‘yar jarida ‘yar kasar Falasdinu daga birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan, bayan da jami’an tsaron gwamnatin kasar suka gayyace ta domin yi mata tambayoyi.

Rasha Hirzallah, wacce ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Falasdinu WAFA, an yi mata tambayoyi ne a wani wurin da ake tsare da su a yankin Ariel na Isra’ila da ke kusa da birnin Ramallah kafin a tsare shi.

Iyalan Hirzallah sun ce jami’an tsaron Isra’ila sun gayyaci ‘yar jaridar, inda bayan isowarta aka shaida mata cewa za ta ci gaba da tsare ta na tsawon sa’o’i 72, ba tare da bayar da wani dalili ko tuhume-tuhume ba.

Hirzallah ‘yar uwa ce ga dan kungiyar gwagwarmayar zaki da aka kashe, Muhammad Hirzallah.

Kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinu ta yi Allah-wadai da tsare Hirzallah a wani bangare na ci gaba da murkushe ‘yan jarida da Isra’ila ke yi.

 

Fassarar: Khadija Muhammad.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Isra’ila ta kame yar jaridar Falasdinawa a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke murkushe ‘yan jarida”