Isra’ila Ta Bayyana Rashin Amincewa Da Shirin Makamshin Nukiliya A Saudiyya

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa manufar Isra’ila tana nan kan bakanta na ganin ba a samu wata kasa daga yankin gabas ta tsakiya da ke aiwatar da shirin makamashin nukiliya ba, yana mai tsokaci kan kalaman ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila a kan batun.
Ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila, Ron Dermer, ya bayyana cewa, Isra’ila za ta amince da bukatar Saudiyya na samun shirin nukiliya na ayyukan farar hula.
Kuma a cewar jaridar “Ynet”, Dermer ya ce Saudiyya na iya samun bukatar ta, ta hanyar China ko Faransa.
Dermer ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Amurka PBS a ziyarar da ya kai birnin Washington inda ya ce: Saudiyya na neman samun damar aiwatar da shirin sarrafa makamashin nukiliya na farar hula.
Ministan kula da tsare-tsare na Isra’ila ya tabbatar da cewa, ba za su taba amincewa da “shirin nukiliya na soja ba.
A halin yanzu dai Isra’ila ce kawai tak mallakan makaman nukiliya a yankin gabas ta tsakiya, wanda ta samar a cibiyoyinta tare da taimakon Amurka.
©VOH