January 28, 2024

​Isra’ila Na Kara Zafafa Hare-Harenta A Gaza Bayan Zaman Kotun ICJ

Rahotanni daga Falastinu na cewa akalla Falasɗinawa 174 Isra’ila ta kara kashewa sannan ta raunata 310 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.

Yahudawan Isra’ila sun yi kisan kiyashi kan iyalai 18 a Zirin Gaza, inda mutum 174 suka rasu tare da raunata 310 a sa’o’i 24 da suka gabata,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa.

“Akwai mutane da dama da har yanzu sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai da kan tituna yayin da masu aikin ceto suka gaza kaiwa gare su,” in ji sanarwar.

 

©VOH

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Isra’ila Na Kara Zafafa Hare-Harenta A Gaza Bayan Zaman Kotun ICJ”