Iran Zata yi Kokarin Inganta Hulda Da Kasashen Afrika

Iran Zata yi Kokarin Inganta Hulda Da Kasashen Afrika
Shugaban Iran Ebrahim Raeisi ya ce kasar na kokarin inganta hulda da kasashen Afirka domin taimakawa kasashen su ci gaba da bunkasa.
A cikin karnuka da suka wuce, kasashen yammacin duniya sun wawashe dukiyar kasashen Afirka ta hanyar amfani da mamaya da kuma kafa mulkin mallaka,” in ji Raeisi yayin da yake jawabi a taron hadin gwiwar kimiyya da tattalin arziki na farko tsakanin Iran da Afirka.
“Amma ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inganta dangantaka da Afirka ba don arzikin wannan yanki ba ne, saboda Iran na neman karfafa alaka da dukkanin al’ummomi ciki har da na kasashen Afirka,” in ji shugaba Ra’isin.
Ya kara da cewa, duk da dimbin takunkumin da aka kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Iran ta yi nasarar samun ci gaba a fannonin fasaha, injiniyanci, likitanci, fasaha, aikin gona, fasahohin halittu, da fasahohin zamani.
Har ila yau Raeisi ya yi ishara da barazanar ta’addanci na gama-gari, da kasashen ketare da Iran da Afirka ke fuskanta, yana mai cewa, “Tare da basirarta da karfinta na dan Adam da na dabi’a, Afirka na iya samun ci gaba mai ma’ana ta hanyar hadin kai, da tsayin daka kan manufofin mulkin mallaka.”