April 4, 2023

​Iran Zata Dauki Matakan Da Suka Dace Kan Sojojin Amurka A Siriya Don Kare Hakkinta A Siriya

 

Jakadan Iran a MDD ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran zata maida martanin da ya dace kan sojojin haramtacciyar kasar Ira’ila (HKI) ko Amurka idan sun taba maslaha da kuma manufofin samuwarta a kasar Siriya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Amir Saed Iravani yana fadar haka a wasikar da ya rubutawa babban sakataren MDD Antonio Guterres. Ya kuma kara da cewa sojojin Iran sun shigo kasar Siriya ne tare da amincewar gwamnatin kasar, sabanin sojojin Amurka.

Iravani ya kara da cewa hare-haren da HKI take kaiwa kan ba zai tafi haka ba tare da daukar fans aba.

A Ranar jumma’an da ta gabata ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan sansanin sojojin kasar Iran a birnin Homs na kasar Siriya inda a nan take suka kashe mai bada shawara ba’irane guda sannan daga bayan wani guda ya yi shahada sanadiyyar raunukan da ya ji a hari na farko.

Jakadan yayi All…wadai da hare-haren da sojojin Amurka suke kaiwa kan wasu wurare a kasar Siriya. Ba bisa ka’ida ba don shigowarsu kasar baya bisa ka’ida.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran Zata Dauki Matakan Da Suka Dace Kan Sojojin Amurka A Siriya Don Kare Hakkinta A Siriya”