January 22, 2023
Iran Za ta Mayar Da Martani Kan Matakin Da Majalisar Turai Ta Dauka Kan Dakarun Kare Juyin Musulunci

Mohammad Qalibaf shugaban majalisar shawarar musulunci ta iran ya bayyana cewa majalisar kasar a shirye take ta dauki matakin da ya dace kan kudurin da majalisar kungiyar tarayyar turai ta fitar na sanyan sunan dakarun kare juyin musulunci na iran daga cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda.
Har ila yau ya fadi cewa makiya suna tunanin cewa dakarun kare juyin musulunci na iran kamar sojojin kasa ne kawai kamar irin na kasashensu, amma gaskiyar lamari shi ne dakarun Karen juyin musulunci da dakarun sakai na basij sun fito ne daga cikin alummamar iran,
Daga karshe shugaban majalisar ya yi kira ga kungiyar tarayyar turai da ta gyara wannan babban kuskure da ta yi tun kafin lokaci ya kure mata, yace kasahen turai su ne suka bawa kungiyar taa’dda ta Da’esh makamai da kayan aiki amma kuma dakarun kare juyin musulunci na iran ne suka yake kuma suka kawo karshenta’addancinsu a yankin baki daya