April 5, 2023
Iran tayi tir da harin HKI a siriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, Nasser Kanaani ya yi Allah wadai da hare-haren da “gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a wasu wurare na Damascus da kewaye a safiyar Juma’a.
Ya ce, abin mamaki da ban takaici ne yadda kasashen duniya ke gum da bakunansu akan wannan dayan aikin da Isra’ila le aikatawa a Siriya.
Abun mamaki a cewarsa Isra’ila na kai wadannan hare-hare a tashoshin jiragen sama na farar hula da ma wuraren zama, yana mai cewa irin wannan shiru shi ne ya karfafa wa gwamnatin Isra’ila gwiwa na mai wa Siriya hare hare..