January 22, 2023

Iran Ta Yi Tir Da Kona Alkur’ani Mai Girma Da Aka Yi A Kasar Sweden.

Kakakin ma’aikatar harkokin waje kasar Iran ya ce; Kona al’kurani mai girma da mutane fiye da biliyan daya da rabi a duniya suke girmamawa, yana nuni ne da siyasar kyamar musulmi da kuma tsokana da cutar da musulmi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Nasir Kan’any din ya kuma ce; Ayyuka maras kyau irin wadannan, ko kadan ba su da alaka da hannun tofa albarkacin baki.

Dr. Kan’any ya kuma ce; Kasashen turawan sun cika duniya da kwakwazo akan batutuwan da su ka shafi kare hakkin dan’adam,amma a lokaci daya su ne a gaba wajen watsa halayyar kiyayya da gaba akan musulmi.

Wani sashe na jawabin kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ya kunshi yin kira gwamantin kasar Sweden da ta hana irin haka faruwa, sannan kuma ta hukunta wadanda su ka cutar da al’ummar musulmi.

A ranar Asbar din da ta gabata ne wani dan siyasar kasar Denmark mai tsattsauran ra’ayin gaba da musulunci da musulmi, ya jagoranci kona alkur’ani a gaban ofishin jakadancin kasar Turkiya dake birnin Stockholm na kasar Sweden.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Ta Yi Tir Da Kona Alkur’ani Mai Girma Da Aka Yi A Kasar Sweden.”