March 12, 2023

​Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Yaki Dabi’ar Tsoron Musulunci Da Kuma Kin Jinin Musulmi.

 

Jakadan kasar Iran kuma wakilinta da din-din din a MDD Amir Saeid Iravani ya yi allawadai da duk wata cutarwa ga mutum bisa akidarsa ko addininsa a duniya, ya kuma yi kira ga kasashen duniya su yaki dabi’an tsoron musulunci da kuma kin jin musulmi a duniya.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto Iravani yana fadar haka a jiya Jumma’a a taron babban zauren MDD don zagayowar ranar fada da ‘tsoron musulunci’ ta kasa da kasa wanda aka saba gudanarwa a ranar 15 ga watan Maris na ko wace shekara.

Jakadan ya kara da cewa : “A yau muna yin allawadai da duk wata tsokana, ko nuna wariya da kuma ayyukan ta’addancin kan musulmi a ko ina suke a duniya. A halin yanzu muna ta ganin yadda yahudawan sahyoniyya suke dirar mikiya a kan al-ummar falasdinu wadanda suka kasance musulmi a kasarsu da yahudawan suka mamaye.”

Sannan a wasu kasashen yamma muna ganin yadda wasu hukumomi a kasashen Turai su ke bada izini ga masu tsattauran ra’ayi na kin jinin musulmi don kona littafin Al-Kur’ani mai girma, abin girmamawa ga musulmi.

Wannan duk da sunan ‘yencin fadin al-barkashin baki a wadan nan kasashe.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Yaki Dabi’ar Tsoron Musulunci Da Kuma Kin Jinin Musulmi.”