May 15, 2023

​Iran Ta Yaba Da Fitowar Dafifin Jama’a A Zaben Turkiya

 

Iran ta taya Turkiyya murnar zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar lami lafiya, tana mai cewa yawan fitowar masu kada kuri’a ya nuna cewa “dimokiradiyya ta yi galaba” a makwabciyar kasa musulma.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kan’ani ne ya bayyana hakan a ranar yau Litinin bayan da sakamakon da aka samu ya nuna cewa za a gudanar da zaben na Turkiyya a zagaye na biyu.

Ya taya al’ummar Turkiyya da masu shirya zabe da kuma jam’iyyun siyasa murna tare da yi musu fatan Alheri.

Kan’ani ya kara da cewa, yawan fitowar masu kada kuri’a a zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Turkiyya da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tare da samun nasarar gudanar da zabe lami lafiya, alama ce ta samun nasara ga demokradiyya a makwabciyar kasar Iran wato Turkiya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran Ta Yaba Da Fitowar Dafifin Jama’a A Zaben Turkiya”