March 23, 2023
Iran ta shigo da masu bada shawara sojojine bisa amincewar gwamnatin siriya.

Kamal Kharrazi jami’in diblomasiyya kuma shugaban majalisar al-amura na musamman na kasashen waje, ya bayyana cewa sojojin kasar Iran a kasar Syriya suna aikin bada shawari ne bisa kuma bukata da kuma amincewar gwamnatin kasar, sabanin kasashen Amurka da Turkiyya wadanda suka shigo da sojojinsu cikin kasar Siriya ba tare da amincewar gwamnatin kasar ba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kharrazi yana fadar haka ne a lokacinda yake jawabi ga ‘yan jaridu a birnin berut na kasar Lebanon. Sannan da aka tambaye shi dangane da lokacinda sojojin Iran zasu bar kasar Siriya, ya ce abinda ya danganci yadda yanayin kasar.