March 8, 2023

​Iran Ta Sha Alwashin Kara Kyautata Matsayin Mata A Kasar Duka Tare Da Takunkuman Da Amurka Ta Dora Mata

 

Zahra Ershadi jakada kuma mataimakin wakilin JMI a MDD ta bayyana cewa gwamnatin JMI zata ci gaba da kyautata matsayin mata a kasar duk tare da takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda gwamnatin kasar Amurka take ci gaba da dorawa kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ershadi tana fadar haka a daren jiya talata a lokacinda take gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD dangane da mata, sulhu da kuma tsaro ta kasa da kasa a birnin News York.

Ta kuma kara da cewa dole ne kasashen duniya su nemi abubuwa na asali wadanda su ke hadda fitinu day aye yake a duniya, don ganin sun kubutar da mata da wahalhalu da suke fadawa cikinsu sanadiyyar wadannan fitinu da yakeyake

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran Ta Sha Alwashin Kara Kyautata Matsayin Mata A Kasar Duka Tare Da Takunkuman Da Amurka Ta Dora Mata”