Iran Ta Nuna Damuwarta Dangane Da Matakin Hana Mata Musulmi Sanya Abaya A Faransa

A wata wasika wacce ta aikawa babban sakataren MDD mataimakiyar shugaba kasa a nan Iran ta nuna damuwarta dangane da yadda wata kotu a kasar Faransa ta tabbatar da shirin ma’aikatar ilmin kasar na hana mata musulmi sanye da abaya shiga makarantun gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministan ilmi na kasar Faransa Gabriel Attal ya bada sanarwa jim kadan kafin a bude makarantun kasar kan cewa ma’aikatar sa ba zata sake amincewa musulmi mata su zo makaranta da rigar abaya ba.
Ensieh Khazali, mataimakin shugaban kasa a cikin al-amuran mata da iyala ta rubuta wasika ga babban sakataren MDD Antonio Gutterre, da shugabar hukumar kari hakkin bi’adama ta MDD sashen kula da mata, Václav Bálek da kuma da kuma shugabar hukumar kula da al-amuran mata CSW Mathu Joyini inda ta bayyana masu cewa matakin da gwamnatin kasar faransa ta dauki sashi hakkin daddaikun mutane ne, kuma take hakkin yencin yin addini ne a kasar ta Faransa, har ila yau takuarawa da kuma tursasawa kanan al-ummu a kasar ta Faransa