January 21, 2023

Iran Ta Jajantawa Ukraine Bayan Hatsarin Helikobta

Ma’aikatar harkokin wajen aksar Iran, ta fitar da wata sanarwa inda take jajantawa kasar Ukraine, bayan mummunan Hatsarin jirgin Helikobta wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 16 ciki har da ministan cikin gidan kasar.

A cikin sanarwar ta ranar Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya isar da sakon ta’aziyya ga gwamnatin Ukraine da kum iyalan wadanda hadarin ya rusa dasu.

Ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a hadarin jirgin.

Akalla mutum 16 ne dai suka mutu a hadarin jirgin mai saukar ungulu a wajen birnin Kiev jiya Laraba, ciki har da Denys Monastyrskyy, ministan cikin gida na kasar da kuwa wasu manyan jami’ai biyu, sai kuma kananen yara uku wadanda jirgin ya rufta kusa da makarantar renonsu.

Tuni dai shugaban kasar Zelensky, ya bayar da umurnin gudanar da binciken kan hadarin jirgin.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Ta Jajantawa Ukraine Bayan Hatsarin Helikobta”