Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Goyon Bayan Gwagwarmayar Palastinawa

Iran ta jaddada aniyarta ta goyon bayan gwagwarmayar da Palastinawa suke yi da gwamnatin Sahayoniyya.
Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da Isma’il Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Hamas da ke Zirin Gaza.
Dama kafin hakan Iran ta ce za ta ci gaba da bayar da karin goyon baya ga al’ummar Palasdinu da kuma gwagwarmayar da suke yi na ‘yantar da yankunan da aka mamaye da kuma kafa gwamnati mai cin gashin kanta mai al-Kudus a matsayin babban birninta.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir Abdollahian ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Asabar tare da babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Islama ta Islamic Jihad, Ziyad al-Nakhalah, inda ya taya shi murnar Sallah Eid-fitr ta karshen watan Ramadan.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da jawabin Eid al-Fitr na Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei dangane da Falasdinu, babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada muhimmancin koma bayan da ‘yan sahyoniyawan ‘yan mamaya, ke ci gaba.