Iran Ta Ja Kunnen Amurka Akan Maganganu Na Tsokana

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a MDD ya aike wa da shuaban kwamitin tsaro da kuma babban magatakardar MDD wasiku da aciki yake yin gargadin akan maganganu na tsokana da Amurka ta yi dangane da shirinta na Nukiliya na zaman lafiya.
Babban mai bayar da shawara akan harkokin tsaron kasar Amurka Jake Sullivan ya bayyana cewa; HKI tana da ‘yancin ta kai wa cibiyoyin Nukiliya na Iran hari,tare da nuna goyon bayan Amurkan akan hakan.
Jakadan na Iran a MDD Amir Sa’id Iruny ya kuma ce wannan maganar ta Amurka tana cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjeniyoyin MDD, tare da yin gargadi akan mummunan sakamakon da yake tattare da hakan.
Shi dai Jake Sullivan ya yi wannan furucin ne a ranar 4 Mayu 2023.
Wasikar ta jakadan na Iran ta kuma kunshi cewa; Furucin na Amurka yana nuni ne da cewa tana da hannu a cikin ayyukan ta’addancin HKI akan masana Nukiliya na Iran da kuma cibiyoyinta.
Har ila yau Amir Sa’id ya yi kira ga Amurka da ta daina watsa karya da gurbatattun bayanai akan shirin Iran na makamashin Nukiliya na zaman lafiya.
Iran din ta jaddada hakkinta na daukar dukkanin matakan da suka dace domin kare cibiyoyinta na Nukiliya.