May 5, 2023

IRAN TA GODE WA SAUDIYYA KAN KOKARINTA NA KWASHE IRANIYAWA DAGA SUDAN.

 

A yayin wani taron manema labarai yau a birnin Tehran na kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Naser Kanaani ya bayyana cewa, Iran tana yin godiya ga irin kokarin da gwamnatin Saudiyya ta yi, wajen kwashe Iraniyawa mazauna kasar Sudan.

Yace Iraniyawa 65 ne aka kwashe, wanda hakan ya gudana ne bisa hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Saudiyya da Iran, Inda Saudiyya ta fitar da su daga Sudan cikin aminci, wanda a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, hakan abin jinjinawa ga gwamnatin Saudiyya.

Da yake tabo batun kara kyautatar alaka tsakanin Iran da Saudiyya a baya-bayan nan, ya ce kasashen biyu suna matakin farko na dawo da huldar da ke tsakaninsu da kuma bude ofisoshin jakadanci ne, yana mai cewa tuni ofisoshin jakadancin Iran guda uku a Riyadh da Jeddah suka fara gudanar da ayyukansu ba tare da wata matsala ba.

Haka nan kuma Saudiyya tana ci gaba da gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka dace domin bude dukkanin ofisoshin jakadancinta a Iran, kuma tuni jami’an na Saudiyya suka iso Iran, kuma ana ci gaba da gudanar da dukanin abin da ya dace kan hakan.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “IRAN TA GODE WA SAUDIYYA KAN KOKARINTA NA KWASHE IRANIYAWA DAGA SUDAN.”