Iran Ta Gargadi Isra’ila Kan Hare-Hare Da Take Kaiwa Kan Syria

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ya yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai a filin jirgin sama na kasa da kasa da ke birnin Aleppo na kasar Siriya, yana mai cewa a karshe za a fuskanci daukar fansa.
Amir Abdollahian ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Damascus babban birnin kasar Syria, inda ya fara wata ziyarar kwanaki biyu, inda ya ce, “Ayyukan laifuka na Isra’ila a yankin ba za su ci gaba da kasancewa ba tare da daukar fansa ba.”
A ranar 28 ga watan Agusta, wani harin bama-bamai da Isra’ila ta kai kan tashar jiragen sama na Aleppo, ya yi sanadiyyar tsayawar dukkanin ayyuka a wurin.
Harin bam din ya zo ne mako guda bayan da sojojin Isra’ila suka kaddamar da hare-hare ta sama kan wasu wurare da ke kusa da birnin Damascus, lamarin da ya yi sanadin jikkata wani sojan Syria da hasarar dukiya.
Bayanin na ministan harkokin wajen Iran dai na a matsayin jan kunne da gargadi ga Isra’ila, kan ayyukan wuce da irin da take yi a kan kasar Syria, wanda kai iya fuskantar mummunan martani ta inda Isra’ila ba ta tsammani.