May 5, 2023

Iran Ta Ce Ko A Jikinta, Fargarbar Amurka Game Da Ziyarar Ra’isi A Siriya

 

Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce ko a jikinta game da fargabar da Amurka ta nuna kan ziyarar tarihi da shugaban kasar Ibrahim Ra’asi ya kai a kasar Siriya.

A cikin wani sabon tuwita kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kan’ani, ba abunda ya damu Iran game da fargabar da Amurka ta nuna.

Furicin na Mista Kan’ani, ya biyo bayan kalaman da mataimakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel, ya yi, inda ya yi ikirarin cewa zurfafa dangantakar dake tsakanin Teheran da Damascus ya kamata ya zama babban abin damuwa, ba kawai ga kawayen Amurka da kasashen yankin ba, a’a har ma ga kasashen duniya baki daya.

Mista Kan’ani ya ce abu ne da ya dace Washington ta fusata saboda ta sha kashi a yankin a hannun ‘yan gwagwarmaya.

Kalamman wannan muguwar gwamnati ba sabon abu ne ba inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.

“Amurka ta bayyana damuwarta game da ziyarar shugaban Iran a Siriya da sakamakonta tare da bayyanata a matsayin munana.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Ta Ce Ko A Jikinta, Fargarbar Amurka Game Da Ziyarar Ra’isi A Siriya”