April 9, 2023

Iran Ta Bukaci Taron Gaggawa Na OIC, Kan Hare-haren Isra’ila A Masallacin Kudus

Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da sakatare janar na kungiyar, ministan harkokin wajen Iran, Hossein AmirAbdollahian, ya ce Iran a shirye ta ke a yi wannan taron duba da halin da ake ciki.

A nasa bangaraen sakataren kungiyar ta OIC, Hossein Ebrahim Taha, ya ce za’a gudanar da taron na OIC ranar Lahadi, na wakilan kasashe mambobin kungiyar a matsakin kwamitin zartarwa domin tattaunawa kan farmakin da Isra’ila ke kaiwa falasdinawa da kuma wurare masu tsarki na musulmi.

Farmakin da ‘yan sanda Isra’ila suka kai masallacin na Al’Aksa ranar Laraba, ya janyo mata toshin Allah-tsine daga kasashen duniya da dama musamman na musulmi.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Ta Bukaci Taron Gaggawa Na OIC, Kan Hare-haren Isra’ila A Masallacin Kudus”