November 30, 2022

Iran Ta Bukaci Kwamitin Tsaro Ya Yi Tir Da Isra’ila Kan Keta Hurimin Siriya

Iran Ta Bukaci Kwamitin Tsaro Ya Yi Tir Da Isra’ila Kan Keta Hurimin Siriya
Jakadan kasar iran na dindin a kwamtin tsaro na Majalisar dinkin duniya Amir Saeid irvan dake halartar taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan halin da ake ciki a gabas ta tsakiya musamman kasar Siriya ya ce matakin da Isra’ila ke dauka na keta hurumin kasar siriya da kai hari da ganagan kan fararen hula da filin saukar jiragen sama da jirgin ruwa dake dauke da kayan agaji ya sabawa dokokin kasa da kasa da na dan adamtaka da ma na majalisar dinkin duniya,
Yace tsaro da zaman lafiya zai tabbata a arewacin kasar siriya ne ta hanyar mutunta hakokin kasar , kuma duk wani matakin soji a arewacin kasar zai kawo cikas sosai a ayyukan jin kai da ake yi a wajen ko ma ya kara tsananta shi.

Daga karshe ya nuna cewa iran tana Allah wadai da masu sace arzikin karkashin kasa na kasar siriya musamman manfetur da dangoginsa a yankunan da sojojin ketare suka mamaye, kuma wannan aikin laifin babban misali ne na keta hurumin kasa mai yanci da kuma kudurin majalisar dinkin duniya

©Hausa TV.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Ta Bukaci Kwamitin Tsaro Ya Yi Tir Da Isra’ila Kan Keta Hurimin Siriya”