Iran Ta Bukaci Amurka Ta Dau Darasi Kan Abinda Ya Faru Da Ita A Shekara Ta 1980 A Hamadar Tabas Na Kasar

Yau shekaru 43 ke nan da rashin nasarar da gwamnatin kasar Amurka ta yi a kokarinta na kwatar jami’an ofishin jakadancinta wadanda suke tsare a birnin Tehran a wani aikin sojen da ta sanyawa sona “Operation Eagle Claw”.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tana fadar haka a wani bayani da tafitar don tunawa da wannan nasarar da JMI ta samu tare da taimakon All..a jim kadan bayan kafa jaririyar gwamnatin musulunci a kasar.
Bayanin ya kara da cewa a ranar 25 ga watan Afrilun shekara ta 1980 ne jiragen yakin Amurka wadanda suka hada da jiragen masu saukar ungulu da kuma wasu jiragen yaki masu kai farmaki suka kushe cikin hamadar Tabas na JMI na nufin kai farami da kuma kifar da JMI har’ila da kuma kubutar da jami’an ofishin jikadancin kasar a Tehran kimani 52 wadanda ake tsare da su saboda ayyukan leken asiri. Amma sai All..ya gamasu da wata guguwa wace ta jawo hatsari da kuma faduwan wasu daga cikin jiragen saman da konewarsu tare da halakar wasu daga cikin sojojin.
Bayanin ya kammala da cewa gas hi shekaru fiye da 40 da faruwar wannan karamar JMI tana kara ci gaba a dukkan bangarorin rayuwa tana kuma hulda da kasashen duniya cikin nutsuwa da zaman lafiya.