Iran Ta Bude Ofishin Jakadancinta A Birnin Riyad A Karon Farko Cikin Shekaru 7 Da Suka Gabata

Shafin labarai na yanar gizo ArabNews na kasar Saudiya ya bayyana cewa tawagar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran zuwa birnin Riyad ta isa birnin ne a ranar Laraba, kuma ta sami tarban jami’an gwamnatin kasar Sudia, a shirye shiryen da kasashen biyu suke yin a maida cikekken huldar jakadanci a tsakaninsu bayan da kasar Cana ta shiga tsakani, kuma ta sasantasu.
Naser Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa tawagogi guda biyu ne suka je kasar Saudia, daya ta je birnin Riyad, dayan kuma ta je birnin Jidda don bude karamin ofishin jakadanci, sannan Iran tana shirin aika da wakilanta a kungiyar kasashen Musulmi ta IOC da ke birnin Jidda.
Masana suna ganin kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu zai warware matsalolin tsari da siyasa a gabas ta tsakiya, daga cikin har da yakin Yemen da kuma Siriya.