Iran: Shugaban Majalisar Koli Ta Tsaron Kasar Zai Ziyarci UAE A Yau Alhamis

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jaridar “Noor News” ta kasar tana fadar haka, ta kuma kara da cewa Shamkhani zai ziyarci UAE ne bisa gayyatar takwaransa na kasar , Tahnoun bin Zayed Al Nahyan. Kuma ana saran zai gana da manya-manyan jami’an gwamnatin kasar wadanda suka hada da tokwaransa Al Nahyan da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar.
Har’ila yau ana saran bangarorin biyu zau tattauna batun farfado da yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar Iran da dauke wa kasar takunkuman tattalin arziki da kuma al-amuran tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Labarin ya kammala da cewa shamkhani zai sami rakiyar wasu jami’an gwamnatin kasar ta Iran a wannan tafiyar.