September 20, 2023

​Iran: Shugaba Raisi Yace Shirin Amurka Na Maida Duniya Karkashinta Ya Kasa Samun Nasara

 

A lokacinda yake jawabi a babban taron MDD karo na 78 shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana shirin shirin Amurka dorawa dukkan kasashen duniya ikonta ya gaza kaiwa ga nasara.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa a halin yanzu wata sabon tsaron duniya na kan haduwa, kuma Iran ba zata amince a sake samun bangarorin gabas da kuma yammacin duniya ba. Sai dai kasar Iran a shirye take ta yi aiki da dukkan kasashen duniya bisa adalci, ba kuma mulkin mallakan da aka samar a karnin da ya gabata ba.

Danganke da makonta kuma, shugaba Ra’isi y ace Iran shirye take ta mika hannu ga duk wata kasa wacce ta mika mata hannun a yankin gabas ta tsakiya.

Sai kuma dangane da kona Alkur’ani mai girma da aka yi ta yi a kasashen Denmark da kuma Sweden, ya ce kona kofin alkur’ani guda ba zai taba kona sakon da ke cikinsa ga bil’adama ba.

Don haka kona al-kur’ani kona dukkan bil’adama ne don sakon da ke ciki na dukkan duniya ne.

Ya ce nuna kiyayya ga addinin musulunci ta kona alkur’ani mai girma ko ta hana mata sanya hijiba ba zai hana wannan addinin shiga cikin zukatan masu son gaskiya a duniya ba.

 

©Htv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: Shugaba Raisi Yace Shirin Amurka Na Maida Duniya Karkashinta Ya Kasa Samun Nasara”