April 22, 2023

​Iran: Ra’isi Ya Taya Shugabannin Kasashen Musulmi Murnar Idin Karamar Sallah

 

Shugaban kasar Iran yana taya shuwagabanni da al’ummar kasashen musulmi murnar zagayowar ranar Sallah karama.

Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ibrahim Raisi, a cikin sakonsa da ya aike wa shugabannin kasashen musulmi, dangane da bukukuwan Sallah mai albarka, ya taya wadannan shugabanni da al’ummomin kasashen musulmi murnar zagayowar wannan rana ta idi mai albarka.

Ya bayyana fatan cewa, tare da albarkar wannan idi da kuma riko da babbar koyarwar Musulunci da kokarin hadin gwiwa, kasashen musulmi za su kyautata hadin kai, don cimma manufofin addini masu rayar da ruhi.

Kamar yadda ya yi fatan samun ci gaba da zaman lafiya a dukkanin kasashen msuulmi da ma sauran kasashe na duniya baki daya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: Ra’isi Ya Taya Shugabannin Kasashen Musulmi Murnar Idin Karamar Sallah”