March 8, 2023

​Iran: Miliyoyin Mutane Sun Gudanar Da Bukukuwan Haihuwar Imam Mahdi(a)

 

Miliyoyin musulmi a nan kasar Iran da wasu kasashen duniyar sun gudanar da bukukuwan haihuwar limami na 12 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) a daren jiya Talata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa miliyoyin mutane ne suka taru a masallacin Jamkaran kilomita 6 daga birnin ilmi a Qum inda suka kwana suna raya daren da wake-wake da ibadoji da kuma raba abinci don nuna farin cikinsu da haihuwar Muhammad dan Hassan Al-Askari (a), wanda mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) sun yi manin cewa an haife shi a ranar 15 ga watan shaabani shekara ta 255 bayan hijira wato shekaru 1,189 da suka gabata.

Sum yi imani kan cewa Imam Mahdi (a) zai bayyana a duk lokacinda All..ta yayi masa izinin bayyana, inda zai cika duniya da adalci bayan

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: Miliyoyin Mutane Sun Gudanar Da Bukukuwan Haihuwar Imam Mahdi(a)”