Iran: Majalisar Kwararru Ta Iran Ta Yi Kira Ga Mutane Su Fito Kwansu Da Kwarkwatarsu Domin Raya Ranar Kudus Ta Duniya.

Majalisar kwararrun ta Iran ta bayyana cewa; Ranar kudus, rana ce da al’ummar musulmin duniya za su nuna fushinsu akan zaluncin masu girman kai da ‘yan sahayoniya.”
Sanarwar ta kuma ce; Bayan kusan cikar wata daya ana azumin Ramadana da yin ibadu, al’ummar musulmi za su sake yunkurawa domin taimakawa al’ummar Palasdinu masu bayar da kariya ga alkiblar farko ta musulmi a matsayin amsa kiran Imam Khumain (r.a) wanda yake kira da a yi gwagwarmaya da’yan sahayoniya da masu goyon bayansu.
Wani sashe na bayanin ya cigaba da cewa; Shakka babu yin gwagwarmaya ta fuskantar zalunci da azzalumai, ita ce hanya mai kaiwa ga samun nasara, domin ta haka ne kungiyoyin gwagwarmaya na Hamas da Hizbullah su ka sami nasar akan HKI wacce take da duk wasu makamai da Amurka ta kera.”
Bugu da kari, bayanin na majalisar ta kwararru ya yi ishara da yadda a shekarar bana ‘yan sahayoniyar su ka tsananta kai wa Palasdinawa hare-hare da kuma yin kuste a cikin masallacin Kudus.