April 30, 2023

Iran: Kwamandan IRGC Ya Bukaci Amurka Da HKI Su Bar Yankin Kudancin Asia

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Alireza Tansiri yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa yankin tekun farisa gidammu ne kuma zamu kareta daga duk wata matsala ta tsaro da ka iya tasowa, amma samuwar sojojin Amurka a yankin Tekun farisa da kuma HKI a yankin suna kara zaman dar-dar a yankin.

Tansiri ya kara da cewa kasancewar sojojin Amurka a yankin Tekun farisa babban matsalace ta tsaron yankin, banda haka kasancewarsu a yankin baya bisa ka’ida, don hada barinsu yankin ya fi tabbatar da tsaro a yabkin kuma sojojin JMI a yankin suna da ikon kiyaye da kuma tabbatar da tsaro a yanking aba daya.

Banda haka Tansiri ya kara da cewa samuwar jiragen yakin na ruwa a tekun farisa hatsari ne ga halittun ruwa a tekun saboda jiragen suna amfani da makamashin nukliya ne, don haka karamin hatsari zai jefa halittun ruwa na ruwan taken cikin hatsari.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: Kwamandan IRGC Ya Bukaci Amurka Da HKI Su Bar Yankin Kudancin Asia”