May 17, 2023

Iran: Kasashen Yamma Masu Goyon Bayan HKI Suna Da Hannu A Ta’asar Da Take Yi A Falasdinu

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya ce kasashen yamma wadanda suke goyon bayan HKI suna da hannu a cikin dukkan ta’asan da ta ke aikatawa a cikin kasar Falasdinu da ta mamaye.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka, a wata sanarwa da ya fitar a jiya talata, inda yake taya al-ummar Falasdinu juyayin cika shekaru 75 da musibar mamayar da yahudawan sahyoniyya suka yiwa kasarsu.

Har’ila yau a karon farko an gudanar da taron taya al-ummar Falasdinu juyayin musibar kafa HKI a kan kasarsu a karon farko a MDD. Yahudawan sun kori miliyoyin falasdinawa daga kasar daga garuruwa kimani 500 a lokacin. Sannan har yanzun tana kan wannan siyasar.

Gwamnatin kasar Burtania ta lokacin kuma yar mulkin mallaka ce ta mikawa yahudawan sahyoniyya kasar Falasdini a cikin watan Mayun shekara 1948, inda suka shelanta kafuwar HKI a kan kasar Falasdinu.

A jawabin da ya gabatar a taron Nakba ko musiba a MDD , shugaban gwamnatin Falasdinawa Mahmood Abbas ya bukaci majalisar ta jingine samuwar HKI a cikin

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: Kasashen Yamma Masu Goyon Bayan HKI Suna Da Hannu A Ta’asar Da Take Yi A Falasdinu”