May 29, 2023

​Iran: Jami’an Tsaron Kan Iyakar Kasar Iran Da Afganistan 2 Ne Suka Yi Shahada A Musayar Wuta Tsakaninsu

​Iran: Jami’an Tsaron Kan Iyakar Kasar Iran Da Afganistan 2 Ne Suka Yi Shahada A Musayar Wuta Tsakaninsu

Jami’an tsaron kan iyakar kasar Iran da Afganistan a lardin Sistan Buluchistan 2 suka yi shahada a lokacinda aka bude masu wuta da misalign karfi 10 na safe a jiya Asabar. Har’ila yau Mutanen biyu fararen hula ne suka ji rauni.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran IRNA na cewa jami’an tsaron kasar Afgansitan ne suka fara budewa Iraniyawa wuta sannan su kuma suka maida martani.

 

Labarin ya kara da cewa an yi fafatawar ne a mashigar kan iyaka na kasashen biyu da ke Sasoli a Zabol cikin lardin Sistan Buluchistan.

 

Majiyar jami’an tsaron kasar Iran a lardin ta kara da cewa a halin yanzu dai ko me ya lafa kuma an kafa kwamiti don bincike da kuma gano musabbabin rikicin.

 

Majiyar gwamnatin Iran ta musanta cewa jami’an tsaron kasar sun kai farmaki da makamai masu linzami kan tashar jiragen sama n Zaranj da ke kasar Afganistan, amma an yi amfani da kanan bindigogi da kuma makaman igwa a fafatawar.

 

A halin yanzu dai gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan rufe kan iyakar kasashen biyu na yankin zuwa nan gaba.

SHARE:
Labaran Duniya, Rahotanni 0 Replies to “​Iran: Jami’an Tsaron Kan Iyakar Kasar Iran Da Afganistan 2 Ne Suka Yi Shahada A Musayar Wuta Tsakaninsu”