May 1, 2023

​Iran: Jami’an Tsaro Sun Kama Y’an Leken Asirin Kasar Faransa Dake Aike Wa Kungiyar Manafukai Ta MKO Bayanai

 

Jami’an tsaro a nan Iran sun kama wasu ma’aikatan leken asiri na kasar Faransa wadanda kuma suke aiki da kungiyar yan ta’adda ta MKO ta munafukai makiya JMI.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa wadanda aka Kaman an taba kamasu a baya amma sai suka sami afwar jagora a sakesu saboda hakan. A aikinsu na barna a baya-bayan nan dai sun samar da wata kungiya don tayar da hankali a tsakanin ma’aikata da malaman makarantu wadanda zasu yi gangami don zagayowar ranar ma’aikata.

Labarin ya kara da cewa Maryam Assadollahi, wacce kuma akewa lakabi da Anisha, da kuma Reyhaneh Ansari duk sun shiga hannu a shekarar da ta gabata saboda aikin leken asiri ga gwamnatin kasar Faransa na kasar. Amma aka sallamesu cikin wata afwar da jagoran juyin juya halin musulunci yayi masu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: Jami’an Tsaro Sun Kama Y’an Leken Asirin Kasar Faransa Dake Aike Wa Kungiyar Manafukai Ta MKO Bayanai”