May 16, 2023

Iran: IRGC Ya Bada Sanarwanashen leken asiri na dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ‘Sepah Fajr’ ya bada sanarwan kama wasu daga cikin shuwagabannin kungiuar yan ta’adda ta ‘Daesh’ reshen Khurasan, a birnin Shiraz na lardin Far daga kudancin kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’in watsa labarai na Sepah Fajr yana bada wannan sanarwan a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa jami’an sashen suna bin duddugin wadannan yan ta’adda tun shekara ta 2019 har zuwa lokacinda suka shiga hannun jami’an na Sepah Fajr a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Kungiyar yan ta’adda ta Daesh dai ita ce ta ammaye kasar Siriya da Iraki a shekara 2014 kuma ta aikata ayyukan ta’addanci da dama a cikin kasar Iran. Na karshensu shi ne wanda dan kungiyar ya shiga hubbaren sha Cherag na birnin Shiraz a lardin Fars ya kuma bude wuta a kan masu ziyara inda ya kashe mutane 13 ya kuma raunata wasu da dama.

Gwamnatin kasar Amurka wacce ta tabbatar da cewa ita ce ta kafa kungiyar yan ta’adda ta Daesh ce ta kashe Janar Shahid Kasim Sulaimani kwamnadan Rundunar Qudus da kuma Mahdi Almuhandis mataimakin shugaban kungiyar Hashdu na kasar Iraki da abokan tafiyansu, wadanda suka kawo karshen ikon Daesh a Iraki, tare da umurnin shugaban kasar Amurka na lokacin Donal Trump.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: IRGC Ya Bada Sanarwanashen leken asiri na dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran ‘Sepah Fajr’ ya bada sanarwan kama wasu daga cikin shuwagabannin kungiuar yan ta’adda ta ‘Daesh’ reshen Khurasan, a birnin Shiraz na lardin Far daga kudancin kasar.”