April 10, 2023

Iran: HKI Ta Yi Kadan Ta Yi Wa Iran Barazana Kawo Mata Hari

 

Babban hafsan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Musawi ya yi watsi da kurari da cika bakin babban hafsan hafsoshin sojan HKI na cewa za su iya kawo wa Iran hari su kadai, yana mai kara da cewa: “Isra’ila ta yi kadan ta yi wa Iran barazana.”

Manjo janar Abdurrahim Musawi ya ce; Irin waccan maganar an yi ta ne saboda a bai wa ‘yan sahayoniyar karfin gwiwa domin magance matsalar da suke fuskanta ta cikin gida.

Manjo janar Abdurrahim Musawi ya kuma ce; A halin yanzu tsarin sahayoniya yana kara nutsewa kuma alamun rushewarsa suna ta fitowa fili.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai hafsan hafsoshin sojan HKI Herzi Havel ya bayyana cewa; A shirye muke mu kai wa Iran hari, Isra’ila tana da karfin da za ta kai hari a kasashen kusa da kuma nesa.”

Haka nan kuma Halevi ya ce a cikin shekaru kadan masu zuwa, za su bunkasa karfinsu na kai harin kandagarko akan Iran, duk da nisan dake tsakani.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: HKI Ta Yi Kadan Ta Yi Wa Iran Barazana Kawo Mata Hari”