October 17, 2021

Iran: Dole Mu Kawo Karshen Makiyan Kasashen Iran Da Azerbaijan

Daga shafin “Hausatv”


Kakakin kwamitin tsaro da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa dole ne a kawo karshen shaidanu wadanda suke son bada dangantaka tsakanin Iran da kasar Azerbaijan.

Majiyar majalisar dokokin kasar Iran ta nakalto Mahmud AbbasZadeh Mishkini yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa irin kokarinda jumhuriyar musulunci ta Iran ta yi wajen yaki da miyagun kwayoyi, ya kai ace idan ba ita ba da dukkan kasashen turai da Kafkas suna fama da matsaloli sanadiyyar miyagun kwayoyi a halin yanzu.

Mishkini ya kara da cewa jumhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar da dubban shahidai a yaki da miyagun kwayoyi a cikin shekaru kimani 40 da suka gabata. Don haka ba zai yi a ce it ace take hada kai da wata kasa don safararta zuwa kasashen Turai kamar yadda shugaban kasar Azerbaijan Elham Aliyof yake fa da ba.

Banda haka kasar Iran tana yanke hukunci mai tsanani ga wadanda aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi wanda hakan ya rage yawan masu safarar irin wadannan miyagun kwayoyi a kasar Iran da ma Afganistan tushen miyagun kwayoyi a yankin.

Daga karshe kakakin kwamitin tsaro da harkokin waje a majalisar dokokin kasar Iran ya ce dole ne aka kawo karshen makiya kasashen biyu makobta, don a zauna lafiya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: Dole Mu Kawo Karshen Makiyan Kasashen Iran Da Azerbaijan”