June 5, 2023

Iran Da Turkiyya Sun Sha Alwashin Zurfafa Dangantakar Dake A Tsakaninsu

Ministocin harkokin waje na kasashen Turkiyya da Iran, sun sha alwashin karfafa alakar dake a tsakaninsu.

Bangarorin sun bayyana hakan ne yayin wata zantawa ta wayar tsarho tsakanin sabon ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, da kuma takwaransa na Iran Hossein AmirAbdollahian, ji ya Lahadi.

Kasashen biyu sun ce zasu karfafa alakar dake tsakaninsu a dukkan fagage, bayan kasancewa dama suna da kyakyawar alaka ta tsawon lokaci a tsakaninsu.

Da yake taya twakwaransa murna, Ministan harkokin wajen Iran, y ace kasashen biyu na da matukar mahimmanci a yankin, wanda kuma ya kamata a karfafa hakan a tsawon wannan sabin wa’adin na shekaru biyar na gwamnatin shugaba Recep Erdogan.

Shi dai M. Hakan Fidan, wanda tsohon shugabar hukumar leken asiri ta Turkiyya ne, a nada shi sabon ministan harkokin wajen Turkiyya ne, inda yam aye gurbin Mevlut Cavusoglu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Da Turkiyya Sun Sha Alwashin Zurfafa Dangantakar Dake A Tsakaninsu”