May 15, 2023

​Iran Da Masar Zasu Maida Huldar Jakadanci A Tsakaninsu Nan Ba Da Dadewa Ba

Maliki ya kara da cewa a halin yanzu wakilan kasashen biyu suna tattaunawa a tsakaninsu a birnin Bagdaza na kasar Iran don tsara yadda zasu maida huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu.

Labarin ya kara da cewa kafin haka ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi a gefen taron Bagdaza a birnin Umman a cikin watan Decemban shekara ta 2022 da ta gabata, inda suka tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi. Kasashen biyu dai sun katse huldar jakadanci a tsakaninsu tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran shekaru fiye da 40 da suka gabata

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran Da Masar Zasu Maida Huldar Jakadanci A Tsakaninsu Nan Ba Da Dadewa Ba”