June 20, 2023

Iran Ce Kadai Ta Shelenta Goyon Bayanta Ga Al-Ummar Falasdinu A fili A Duniya

 

Shugaban kungiyar Jihadul Islami ta falasdinawa masu gwagwarmaya da makami don kwatar kasarsu Falasdinu daga hannun yahudawan Sahyoniyya yan mamaya Ziyad al-Nakhaleh ya yabawa JMI kan irin goyon bayan da take bawa al-ummar Falasdinu, sannan ita ce kasa tilo a duniya wacce ta bayyana goyon bayan gwagwarmaya da makami wanda kungiyoyin falasdinawa suke yi da HKI a kasar falasdinu da ta mamaye.

Ziyad Nakhala ya bayyana haka ne a hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Al-Alam da harshen larabci a nan Iran.

Shugaban kungiyar Jihadul Islami wanda ya jagoranci tawagar Falasdinawa zuwa kasar Iran tun makon da ya gabata ya kara da cewa shuwagabannin kungiyarsa da ta kungiyar Hamas sun gana da manya-manyan jami’an dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran, wanda ya nuna a fili na irin goyon bayan da JMI take bawa al-ummar Falasdinu a gwagwarmayansu da HKI.

Har’ila yau shugaban bangaren siysa na kungiyar Hamasa Isma’ila Haniyya ya bayyana cewa tawagarsa ta gana da shugaban majalisar koli ta harkokin tsaro na kasar Iran wanda ya kara tabbatar masu da cewa hanayar gwagwarmaya da makami ne kadai mafita daga mamayar da HKI takewa kasar Falasdinu fiye da shekaru 70 da suka gabata.

 

©Hausa Tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran Ce Kadai Ta Shelenta Goyon Bayanta Ga Al-Ummar Falasdinu A fili A Duniya”