June 3, 2024

Iran barazana ce ta yanar gizo ga kasashen Yamma da Yahudu da kasashen Gulf

Ra,ayin

Daga:CATHERINE PEREZ-SHAKDAM   3/06/ 2024

Masu zanga-zangar sun kona tutar Isra’ila da Amurka a Tehran, a farkon wannan shekarar. Barazana ta yanar gizo ta Iran tana damun Al’ummar Yahudu, wanda Iran ke kai hari a matsayin wani bangare na babban Manufarta dake kunshe a cikin takenta mai ban tsoro: ‘Mutuwa ga Amurka, Mutuwa ga Isra’ila,’

Ayyukan yanar gizo na Jamhuriyar

Musulunci, da ke da nufin tarwatsa manyan biranen Yamma, da kai hari ga al’ummar Yahudawa, da kuma barazana ga kasashen GCC, na wakiltar wata barazana ta zahiri ga tsaron kasa.

A cikin duniyar da ke da alaƙa ta yau, barazanar da muke fuskanta ba ta zahiri ba ce kawai amma har da na dijital, masu ruɗi, da kuma mamayewa.

Daga cikin wadannan barazanar, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fito fili a matsayin abokiyar gaba da wayo. Nazari na baya-bayan nan, kamar rahoton watan Mayu na 2023 na Majalisar Atlantika, ya nuna yadda Iran ke haɓaka damar Intanet da nufin tarwatsa ayyukan jihohi da kuma kai hari ga mutane a duniya. Wannan barazana ta shafi al’ummar yahudawa, wanda Iran ke kai hari a matsayin wani bangare na babban manufarta, wanda ke kunshe cikin takenta mai ban tsoro: “Mutuwa ga Amurka, Mutuwa ga Isra’ila.

 

Mai Fassarar:Hadiza Mohammed.

© Iran News

SHARE:
Tsokaci 0 Replies to “Iran barazana ce ta yanar gizo ga kasashen Yamma da Yahudu da kasashen Gulf”