November 19, 2021

Iran: Bai kamata a bar makobtan Afghanistan da matsalolin da Amurka ta jefa kasar ciki ba

Daga shafin Hausatv


Jakadan kasar Iran a MDD ya bukaci a kasashen duniya su taimakawa kasar Afgansitan sabo da warware matsalolin da Amurka ta barwa kasar bayan shekaru fiye da 20 da mamayar kasar ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Majid TakhtRavanchi yana fadar haka a taron kwamitin tsaro na MDD a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa bai kamata a bar makobtan kasar Afganistan da matsalolin da Afganistan take fama da su ba.

 

Jakadan ya kara da cewa a halin yanzu mutanen kasar Afgansitan kimani miliyon 4 ne suke rayuwa a kasar Iran mafi yawansu ‘yan gudun hijira ne, sanadiyyar rikicin da Amurka ta haddasa a kasarsu tsakanin shekera 2001 2021.

Ya ce bayan ficewar Amurka daga kasar ba shiri a cikin watan Augustan da ya gabata dubban mutanen kasar ne suka shiga kasar Iran. Sannan idan ba’a dauki matakan da suka dace ba, wannan adadin zai karu saboda rike kudaden kasar wanda Amurka ta yi bayan da Taliban ta karbi iko da kasar.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Iran: Bai kamata a bar makobtan Afghanistan da matsalolin da Amurka ta jefa kasar ciki ba”