April 22, 2023

​Iran: Ayatollah Khamenei Ya Jagoranci Sallar Idin Karamar Sallah A Tehran

 

A Tehran babban birnin kasar Iran , jama’a sun taru a masallacin Imam Khumaini domin gudanar da sallar Idi. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranci sallar.

A cikin jawabin da jagoran ya gabatar, ya bayyana cewa, idin karamar sallar na a matsayin mai kammala babbar tarbiyar da muminai suka samua cikin watan Ramadan.

Sannan ya bayyana cewa, dole ne musulmi su zama masu amfana da wannan babbar dama da Allah ya ba su wajen samun kusanci da shi, domin tsarkake ruhi, ta hanyar yin biyayya ga Allah a dukaknin abin da ya yi uamrni da kuma nisantar abin da ya yi hania kansa.

Ya kuma kirayi al’ummar kasar Iran das u zama cikin fadaka, su kuma hada kansu domin tunkarara makircin makiya da ke neman rusa musu kasa, wadda take da cikakken ‘yanci na siyasa.

Musulmi a Iran da sauran wasu kasashe na gudanar da bukukuwan karamar Sallah a karshen azumin watan Ramadan, bayan an ga jinjirin watan Shawwal a daren jiya.

Kasashen duniyar musulmi da dama ne suka hada da Saudiyya, Qatar, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa, Yemen, Falasdinu, Siriya, da Masar, sun sanar da cewa a jiya Juma’a ne a matsayin ranar idi.

Yayin da Iran, Oman, Pakistan, Indonesia, Malaysia da kuma Iraki suna gudanar da bukukuwan Sallar Idi a ranar Talata.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Iran: Ayatollah Khamenei Ya Jagoranci Sallar Idin Karamar Sallah A Tehran”